audio
audioduration (s) 0.06
109
| transcription
stringlengths 1
1.01k
|
---|---|
Afi 6 |
|
Biyayya da Ƙauna |
|
Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai. |
|
Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don al'amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.” |
|
Ku ubanni, kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji. |
|
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya, da hali bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya ɗaya, Almasihu kuke yi wa ke nan, ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai kamar bayin Almasihu masu aikata abin da Allah yake so, da zuciya ɗaya, kuna bauta da kyakkyawar niyya domin Ubangiji kuke yi wa, ba mutane ba. |
|
Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi. |
|
Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku sani, shi wanda yake Ubangijinsu da ku duka, yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe. |
|
Makaman Allah Duka |
|
A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa. |
|
Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis. |
|
Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu. |
|
Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage. |
|
Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku, shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku. |
|
Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita. |
|
Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah, a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. |
|
A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a. |
|
Ni ma ku yi mini, domin in sami baiwar yin hurci, in yi magana gabagaɗi, in sanar da asirin bishara, wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. |
|
Ku dai yi mini addu'a, duk sa'ad da nake yin bisharar, in bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi. |
|
Gaisuwa |
|
A yanzu kuwa, don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da nake a ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen ɗan'uwa, amintaccen mai hidimar Ubangiji, zai sanar da ku kome. |
|
Na aiko shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, ya kuma ƙarfafa muku zuciya. |
|
Salamar Allah Uba da ta Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata ga 'yan'uwa, tare da ƙauna game da bangaskiya. |
|
Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa. |
|
Yah 4 |
|
Yesu da Wata Basamariya |
|
To, da Ubangiji Yesu ya sani dai Farisiyawa sun ji labari yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yahaya (ko da yake dai ba Yesu kansa yake yin baftisma ba, almajiransa ne), sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili. |
|
Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya. |
|
Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya, wanda ake kira Saikar, kusa da yankin ƙasar da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu. |
|
Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. |
|
Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. |
|
Wajen tsakar rana ce kuwa. |
|
Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. |
|
Yesu ya ce mata, “Sa mini ruwa in sha.” |
|
Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci. |
|
Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” |
|
(Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa). |
|
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.” |
|
Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. |
|
To, ina ka sami ruwan nan na rai? |
|
Ashe, ka fi ubanmu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da 'yayansa, da dabbobinsa, suka sha ruwanta?” |
|
Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sāke jin ƙishirwa. |
|
Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. |
|
Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.” |
|
Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, kada kuma in riƙa zuwa har nan in ɗiba.” |
|
Sai Yesu ya ce mata, “Je ki, ku zo da mijinki.” |
|
Sai matar ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” |
|
Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji, don kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. |
|
A nan kam kin yi gaskiya.” |
|
Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne. |
|
Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan. |
|
Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada yake.” |
|
Sai Yesu ya ce mata, “Uwargida, ki gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima, Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa yake. |
|
Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. |
|
Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. |
|
Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.” |
|
Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. |
|
Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.” |
|
Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganan nan da yake.” |
|
Nan take almajiransa suka dawo. |
|
Suka yi mamakin ganin yana magana da mace. |
|
Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me kike bukata?” |
|
ko, “Don me kake magana da ita?” |
|
Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane, “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! |
|
Shin, ko wannan shi ne Almasihu?” |
|
Sai suka fito daga garin suka nufo shi. |
|
Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.” |
|
Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.” |
|
Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?” |
|
Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. |
|
Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? |
|
Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi. |
|
Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. |
|
A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’ |
|
Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. |
|
Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.” |
|
Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” |
|
Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. |
|
Ya kuwa kwana biyu a nan. |
|
Waɗansu kumma da yawa fiye da na dā suka ba da gaskiya saboda magana tasa. |
|
Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.” |
|
Yesu Ya Warkar da Ɗan Bafada |
|
Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili. |
|
Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu. |
|
Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin. |
|
Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. |
|
A Kafarnahum kuwa akwai wani bafada wanda ɗansa ba shi da lafiya. |
|
Da jin cewa Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkar da ɗansa, don yana bakin mutuwa. |
|
Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” |
|
Sai bafadan nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.” |
|
Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” |
|
Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa. |
|
Yana cikin tafiya sai ga barorinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka a raya yake.” |
|
Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. |
|
Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya na rana zazzaɓin ya sake shi.” |
|
Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” |
|
Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama'ar gidansa duka. |
|
Wannan kuwa ita ce mu'ujiza ta biyu da Yesu ya yi, bayan Komowarsa ƙasar Galili daga ƙasar Yahudiya. |
|
1Kor 5 |
|
Hukunci a kan Fasikanci |
End of preview. Expand
in Dataset Viewer.
README.md exists but content is empty.
- Downloads last month
- 43