text
stringlengths
0
727
shin an saukar da alƙur'ãni ne a kansa a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)
ã'a sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu kuma sã'ar tã fi tsananin masĩfa kuma ta fiɗãci
kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda allah yake mai halaka su kõ kuwa mai yi musu azãba azãba mai tsanani suka ce dõmin nẽman hanzari zuwa ga ubangijinku kuma tsammãninsu sunã yin taƙawa
waɗannan sunã da abinci sananne
saukar da littafi daga allah mabuwãyi mai hikima yake
ka ce wanda ya kasance maƙiyi ga jibirilu to lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin allah yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi kuma da shiriya da bishãra ga mũminai
to lalle ne ubangijinka haƙĩƙa mai tausayi ne mai jin ƙai
ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai
gõdiya ta tabbata ga allah ã'a mafi yawansu ba su sani ba
kuma lalle ne haƙĩƙa mun jujjũya a cikin wannan alƙur'ãni daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne su bi sharĩ'a) kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli
kuma haka ake fitar da ku
bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba fãce idan allah ya so
kuma idan aka ce musu ku yi ĩmãni da abin da allah ya saukar sai su ce muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa alhãli kuwa shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na attaura) ka ce to don me kuke kashe annabãwan allah gabãnin wannan idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya
da yinin da aka yi alkawarin zuwansa
shin yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne
kuma idan kun kyautata kuma kuka yi taƙawa to lalle ne allah yã kasance ga abin da kuke aikatãwa masani
kuma allah ne ya sanyã muku inuwa daga abin da ya halitta kuma ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu kuma ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku
kuma allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne
daga sharrin mai sanya wasuwãsi mai ɓoyewa
kuma bãbu wani abinci sai daga (itãcen) gislĩn
waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya)
zuwa ga fir'auna da majalisarsa sai suka kangara alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya
a lõkacin da kake cẽwa ga mũminai shin bai ishe ku ba ubangijinku ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku
kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba
shin kuma ba su yi tafiya ba a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance
ashe ba ka dũba ba zuwa ga ubangijinka yadda ya miƙe inuwa
lalle ne jĩ da gani da zũciya dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya
sai ya yi nufin fitar da su daga ƙasar sai muka nutsar da shi shi da wanda yake tãre da shi gabã ɗaya
yanã fitar da mai rai daga matacce kuma yanã fitar da matacce daga mai rai kuma yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta kuma haka ake fitar da ku
to kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya
kuma bã mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa kuma a wurinmu akwai wani littãfi wanda yake magana da gakiya kuma sũ bã a zãluntar su
daga wane abu (allah) ya halitta shi
sa'an nan kuma muka darkãke wasu
to ka yi tasbihi game da gõde wa ubangijinka kuma ka nẽme shi gafara lalle shi (ubangijinka) ya kasance mai karɓar tũba ne
kuma muka ɗaure a kan zukãtansu a lõkacin da suka tsayu sa'an nan suka ce ubangijinmu shĩ ne ubangijin sammai daƙasa bã zã mu kirãyi waninsa abin bautawa ba
sabõda haka ku gudu zuwa ga allah lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku mai bayyanannen gargaɗi
_alama
kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci alhãli a wurinsu akwai attaura a cikinta akwai hukuncin allah sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan waɗannan bã muminai ba ne
kuma suka ce kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã dõmin ka sihirce mu da ita to baza mu zama sabõda kai mãsu ĩmãni ba
kuma muka sanya wata tõshiya a gaba gare su da wata tõshiya a bãyansu sabõda haka muka rufe su sai suka zama bã su gani
an ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su a rãnar ¡iyãma
suka ce sun ɓace mana ã'a ba mu kasance munã kiran kõme ba a gabanikamar wancan ne allah yake ɓatar da kãfirai
wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo sunã mãsu sallamãwa
kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce kaitonku sakamakon allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni kuma ya aikata aikin ƙwarai kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai ha ƙuri
dukkansu munã taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar ubangijinka kuma kyautar ubangijinka ba ta kasance hananna ba
allah ya gina ta
sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta lãhira bãbu musanyãwa ga kalmõmin allah
sabõda haka suka zamanto kamar duwatsu ko mafi tsananin ƙeƙashewa kuma lalle ne daga duwãtsu haƙĩka akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi kuma lalle ne daga gare su haƙĩƙa akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi kuma lalle ne haƙĩƙa daga gare su haƙĩƙa akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron allah kuma allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa
lalle ne allah ne mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu
kuma suka ce mẽ ya sãme mu bã mu ganin waɗansu mazãje mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai
danna ka kalli alkawarin ka da hidimomin ka
waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu)
kuma waɗanda suke cẽwa ya ubangijinmu ka karkatar da azãbar jahannama daga gare mu
kuma wanda ya bi allah da taƙawa (allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa
a rãnar da dũkiya bã ta amfãni kuma ɗiya bã su yi
lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen aljanna)
sa'an nan a lõkacin da ya fãɗi ya ce lalle ne idan ubangijina bai shiryar da ni ba haƙĩƙa inã kasancẽwa daga mutãne ɓatattu
kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin ubangijinsu
ya ce yã ubangijina
kuma suka ce yã ubangijinmu
lalle ne shi ya kasance alfãsha da abin ƙyãma kuma ya mũnana ya zama hanya
sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi
abin da suke hukuntãwa yã mũnanã
dã yã kasance wata siffar dũniya ce makusanciya da tafiya matsakaiciya dã sun bĩ ka kuma amma fagen yã yi musu nĩsa kuma zã su yi ta yin rantsuwa da allah dã mun sãmi dãma dã mun tafi tare da ku
lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba
rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu ku ɗanɗani shãfar wutar saƙar
dã yã kasance wata siffar dũniya ce makusanciya da tafiya matsakaiciya dã sun bĩ ka kuma amma fagen yã yi musu nĩsa
kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba kuma dã ba a kashe su ba (wannan kuwa) dõmin allah ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu
sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne
kuma wanda ya nufi lãhira kuma ya yi aiki sabõda ita irin aikinta alhãli kuwa yanã mũmĩni to waɗannan aikinsu ya kasance gõdadde
kuma lalle ne haƙĩƙa mun sanya waɗansu masaukai a cikin sama kuma muka ƙawãta ta ga masu kallo
kuma lalle ne cẽwa allah yanã tãre da mũminai
ashe ba mu sanya ƙasa shimfiɗa ba
kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ ku ƙaryata (shi)
sa'an nan muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare mu karɓa mai sauƙi
waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya kuma azãba da gãfara
kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsõro ya je musu sai su wãtsa shi dã sun mayar da shi zuwa ga manzo da ma'abũta al'amari daga gare su lalle ne waɗanda suke yin bincikensa daga gare su zã su san shi
yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi
lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da lãhira
da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)
kuma lalle mun aiki waɗansu manzanni a gabãninka zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji bayyanannu sa'an nan muka azabtar da waɗanda suka yi laifi kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu
@ title menu
jerin shaidar fanel
to amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka a cikin wani lambu
kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi kuma kunã ĩmãni da allah kuma dã mutãnen littãfi sun yi ĩmãni lalle ne dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su
kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya ya sanya muku (albarka) ga gõnaki kuma ya sanya muku koguna
lalle nĩ nã ji tsõron ka ce ka rarraba a tsakãnin banĩ isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba
sai muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri
idan (alƙur'ãni) ya kasance daga allah ne sa'an nan kun kãfirta a game da shi wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)
kuma suka ce shin idan mun kasance ƙasũsuwa da niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe lalle ne mũ haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa
da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa
da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma mun saukar da ambato zuwa gare ka dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su kuma don ɗammãninsu su yi tunãni
ka karkatar da azãbar jahannama daga gare mu
idan ya so zai tafi da ku kuma ya zo da wata halitta sãbuwa
waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa kuma ãƙibar kãfirai ita ce wuta
lalle ne shi azzãlumai bã zã su ci nasarã ba
ashe allah bai zama mabuwãyi ba mai azãbar rãmuwa
tsarki ya tabbata a gare shi shĩ ne allah makaɗaici mai tĩlastãwa
kuma bã ni tambayar ku wata ijãra ijãrãta ba ta zama ba fãce daga ubangijin halittu